Neja: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 19 A Masallaci

Labarin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar Shugaban karamar hukumar Mashaegu a jihar Alhaji Alhassan Isah, ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane 19 tare da yin garkuwa da 15 a Mazakuka, Kulho, Adogon Malam da kewaye.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana hakan ne rsnar Talata 11 a lokacin da ya gurfana gaban kwamitin bincike na shari’a da gwamnatin jihar ta kafa kan kashe-kashen.

Ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutane 19 a cikin masallaci yayin harin da suka kai ranar 25 ga watan Oktoba Bara. Isah ya ce an kuma kashe mutane biyu da ke kusa da masallacin, yayin da aka yi garkuwa da wasu 15 a nan take.

Shugaban ya ce daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ya mutu ne saboda kaduwa sannan ‘yan bindigar suka kashe wasu takwas a daji. Ya kuma shaida wa hukumar cewa an saki mutane 11 da aka sace bayan biyan kudin fansa da iyalansu suka yi.

Labarai Makamanta