Neja: Sun Nutse Ruwa A Yunƙurin Tsere Wa ‘Yan Bindiga

Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kaddamar da hari a Karamar Hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Wani mazaunin yankin ya tabbatarwa da Aminiya cewa an yi awon gaba da mata da kananan yara da dama a harin da aka kai yankin Gurmana a Karamar Hukumar ranar Asabar.

Da yake tabbatar da harin, wani shugaba a Kungiyar Matasa ta Garin Shiroro, Sani Abubakar Yusuf Kokki ya ce wasu daga cikin wadanda harin ya ritsa da su da suka yi kokarin tserewa sun nitse a kogin Kaduna.

Ya ce ‘yan bindigar sun yi ta harbi a sararin samaniya domin su jefa tsoro a zukatan mutane, sannan suka harbi wasu.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, yunkurinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Neja, Wasiu Abiodun kan batun ya ci tura saboda bai amsa kira da rubutaccen sakon da aka tura masa ba.

Wannan ne dai karo na uku da ake samun rahoton kai hari a jihar ta Neja cikin kasa da mako guda.

Ko a ranar Larabar da ta gabata sai da wasu ‘yan bindiga sanye da kakin sojoji suka sace dalibai da malaman Makarantar Sakandiren Gwamnati dake Kagara su 42.

Labarai Makamanta