Neja: Sarkin Kagara Ya Kwanta Dama

Rahotanni daga Masarautar Kagara ta Jihar Neja na bayyana cewar Mai martaba Sarkin Kagara na Alhaji Salihu Tanko ya rasu, da sanyin safiyar yau.

Tsohon Sanatan Kaduna, @ShehuSani ya tabbatar da rasuwar Sarkin a shafinsa na twitter a ranar Talata.
“Na samu labarin bakin ciki game da rasuwar Sarkin Kagara na Jihar Neja, Alhaji Salihu Tanko. Allah Ya ba shi gidan Aljanna firdausi. Amin.

Inna lillahi wainna Illayhir rajiun.” An nada Salihu Tanko a matsayin Sarki na 16 na Tegina a 1971.

A ranar 1 ga Janairun 1982, an nada shi a matsayin Hakimin Kagara na biyu tare da matsayi mai daraja ta biyu domin ya gaji Alh Ahmadu Attahiru wanda ya rike mukamin har zuwa rasuwarsa a watan Nuwamba, 1981.

A ranar 1 ga Nuwamba 1991, Alh Salihu Tanko ya samu daukaka zuwa matsayin Sarki mai daraja ta daya a hannun Gwamnan jihar Neja Kanal Lawan Gwadabe.

Rasuwar tashi na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan Bindiga ke cigaba da addabar yankin da muggan hare – hare, indai jama’a ba su manta ba a “yan kwanakin baya ne ‘yan Bindiga suka sace tulin ɗalibai a makarantar kwana ta maza dake Kagara, bayan ceto ɗaliban ne ‘yan Bindiga suka ƙara kai hari yankin Arewacin inda suka hallaka mutane da dama.

https://hausa.legit.ng/1405308-da-dumi-dumi-sarkin-kagara-garin-da-aka-sace-dalibai-da-malamansu-ya-rasu.html

Labarai Makamanta