Neja: Hatsarin Kwale-Kwale Ya Lakume Rayukan Mutum Bakwai

Labarin dake shigo mana daga Mina babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Mutum uku ‘yan gida daya na cikin mutane bakwai da suka mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a kauyen Zhigiri na karamar hukumar Shiroro da ke jihar.

Jaridar ThisDay, wadda ta rawaito wannan labari, ta kara da cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi da maraice.

Cikin wadanda suka mutu har da mata guda biyu na wani mutum mai suna Mallam Muazu Babangida da kuma dansa guda daya.

Sai dai ba a san sauran mutanen da suka mutu ba.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne lokacin da mutanen suke kan hanyarsu ta zuwa kauyen Dnaweto domin halartar bikin radin suna.

Hukumomi ba su ce komai a kan batun ba kawo lokacin rubuta wannan labarin, sai dai sanarwar da kungiyar Coalition of Shiroro Association ta fitar ranar Talata ta tabbatar da faruwar lamarin.

Labarai Makamanta