Neja: Gwamnati Ta Haramta Cinikin Babura

Labarin dake shigo mana daga Minna Babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Sani Bello ta haramta siyar da babura a cikin jihar.

Babban sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane, wanda ya sanar da hakan a cikin wani jawabi a ranar Asabar, ya ce hukuncin ya biyo bayan matsalolin rashin tsaro da ake fama da su a wasu yankunan jihar.

Ya kuma ce an dauki matakin ne saboda bukatar da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke gabatarwa na neman a basu babura a matsayin fansa.

“Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya yi umurnin haramta siyar da babura a fadin jihar.” Matane ya ce baburan da haramcin ya shafa sun hada da Bajaj, Boxer, Qiujeng, Honda ACE, Jingchen da sauransu masu dauke da injin mai karfin 185cc.

Sakataren ya ci gaba da bayanin cewa gwamnatin jihar ta kara wannan matakin ne da nufin rage ayyukan miyagu a jihar. Ya bayyana cewa gwamnatin ta lashi Takobin magance hargitsin da yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke haddasawa a wasu yankunan jihar sannan ta jadadda jajircewarta na fitar da jihar daga kowane irin barazana na tsaro.

“Gwamnati na sane da rashin walwalar da matakin zai haddasawa mutane, amma an dauki matakin ne saboda ra’ayin jihar sannan ya roki dillalan babura a fadin jihar da su bayar da hadin kai a kan umurni.”

Labarai Makamanta