Neja: An Sako Ɗaliban Makarantar Kagara

Labari da ke shigo mana yanzu daga Minna babban jihar Neja shine na sako wadanda aka yi garkuwa da su a makarantar sakandaren Kagara.

Amma kuma sakatariyar yada labarai ta jihar ta ce akwai wasu kalubale don haka bai kamata a fara murna ba tukuna a jira komai ya kammala tukuna.

An sako su a sa’o’in farko na safiyar ranar Asabar ɗin amma a yanzu suna kan hanyarsu ta zuwa Minna babban birnin jihar Neja cikin kulawar jami’an tsaro.

Majiya mai karfi ta sanar da cewa a halin yanzu wadanda aka sace suna kan hanyarsu ta zuwa Minna kuma nan da sa’o’i kadan za su isa babban birnin.

Babbar sakatariyar yada labarai, Mary Nole-Berje, ta ce duk da ta samu labarin sako wadanda aka sace, har yanzu gwamnati bata sanar da ita ba a hukumance saboda dalilan tsaro.

“Na ji labarin sako su amma gwamnati bata sanar da ni ba saboda akwai wasu kalubale.” “Idan sun iso Minna lafiya kalau kuma Gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello ya karbesu ne zamu yarda kuma mu fara murna,” tace.

Labarai Makamanta