NCDC Ta Tafka Karya A Adadin Masu CORONA A Jihar Zamfara – Matawalle

Gamnatin jihar Zamfara ta bayyana rashin amincewarta da alkaluman da NCDC ta fitar na wadanda su ka kamu da cutar Coronavirus a jihar a ranar Litinin.

A jiyan NCDC dai ta sanar da cewa sabbin mutane 10 sun kamu da cutar Corona a jihar ta Zamfara.

Sai dai yau kwamishinan lafiya a jihar Zamfara, Alhaji Yahaya Kanoma ya shaidawa manema labarai cewa mutane biyu ne aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar Corona a jihar Zamfara Jiya Litinin amma NCDC sukace 10.

Kwamishinan yace tuni gwamnatin jihar Zamfara ta ankarar da NCDC a kan kuskuren da ta yi tare da neman ta gyara cikin gaggawa.

Yace Mun yi matukar mamaki bayan ganin alkaluman NCDC sun nuna cewa an samu sabbin mutane 10 da su ka kamu da cutar Corona a Zamfara bayan mutane biyu kacal mu ka sani.

Sakamakon da aka dawo ma na da shi daga NCDC ya nuna cewa mu na da jimillar mutane 76 da ke dauke da cutar, an sallami 45 daga cikinsu, 26 su na cibiyar killacewa, mutane biyar sun mutu, yace ba mu san inda NCDC ta samo karin mutane 8 da su ka sanar ba.

Related posts