Nasarawa: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Marasa Lafiya

Rahotanni daga Lafiya babban birnin Jihar Nasarawa na bayyana cewar wasu ‘yan Bindiga sun afka cikin wani Asibiti inda suka yi garkuwa da marasa lafiya da ma’aikatan asibitin, sannan suka buƙaci kuɗin fansa.

Daga bisani bayan wani artabu rundunar ‘yan Sanda ta yi nasarar cafke mutum biyu cikin gungun ‘yan Bindigar inda ba tare da wani ɓata lokaci ba aka gurfanar da su gaban ƙuliya domin girbar abin da suka shuka.

Mutane da ake zargi ‘yan Bindiga ne Abdullahi Danshoho da Illiyasu Salleh, sun bayyana matsayinsu a sace wasu marasa lafiya biyu da wata ma’aikaciyar jinya a wani asibiti a Jihar Nasarawa.

Wadanda ake zargin tare da ‘ya’yan kungiyar su sun kai mamaya asibitin Kunwarke da ke Lafia, Jihar Nasarawa, wani lokaci a watan Nuwamban 2020 sannan kuma suka sace marasa lafiya biyu da wata ma’aikaciyar jinya.

An yi zargin cewa sun karbi kudin fansa naira miliyan 6 kafin su sako mutanen da suka sace.

Mun zabi yin garkuwa da mutane ne saboda shine hanya mafi sauki na samun kudi, inji su.

Rundunar ‘yan Sanda karkashin jagorancin DCP Abba Kyari ne suka yi nasarar kama Danshoho da Salleh a kwanan nan.

Danshoho mai shekaru 25 wanda ke da aure da yara hudu, ya bayyana cewa shi direban babbar mota ne amma ya shiga satar mutane saboda baya samun kudi sosai daga aikin.

“Na gama NCE a 2020 amma har yanzu ban karbi sakamako na ba. Na zama direban babbar mota amma abubuwa sun yi wuya. Na hadu da abokina, Illiyasu (Salleh), wani lokaci a cikin Satumba 2020 kuma ya gaya mani hanya mai sauƙi na samun kuɗi.

Ya gaya min cewa satar mutane ita ce kawai mafita. Ya ce min in nemi masu kudin da za mu sace.” Ya ce da shi aka sace mutane biyar – na karshen shine a watan Disamba – ciki har da sace makwabcinsa da ya ki ba shi kudi.

Ya bayyana cewa ya ba da bayanan mutumin ga Illiyasu wanda ya shirya sace shi, ya kara da cewa ya samu N100,000 kaso daga kudin fansar da aka biya.

Danshoho ya bayyana cewa, “Illiyasu ne ya shirya aikin na biyu da aka yi cikin nasara.

Wannan asibitin shine inda muke yawan zuwa yin magani. Aikina shine in tabbatar cewa shugaban asibitin yana nan.

A ranar da muka kai farmaki, na tabbata cewa yana asibiti. Abin takaici, ya sami damar tserewa. Wannan shine dalilin da yasa suka yanke shawarar sace marasa lafiya.

“Bayan wasu kwanaki, sun ba ni N100,000 a matsayin kasona. Ban yi korafi ba saboda sun fada min cewa marasa lafiyar manoma ne kuma ma’aikaciyar jinyar ta fito ne daga dangin talakawa.

“Bayan mako guda, na kawo aiki na uku. Abokina ne kuma mun saba zama tare. Na yanke shawarar yin garkuwa da shi ne saboda na tabbata iyayensa za su iya biyan kudin sakin nasa.

Sun biya miliyan 1.5 kuma na samu N100,000 a matsayin rabona. Lokacin da ya dawo gida rashin lafiya ne na yi nadamar abinda na aikata.

Na yi amfani da wani bangare na kudina wajen biyan basussuka a makarantar domin in samu takardar shedata.”

Salleh, mai shekaru 24, ya ce ya shiga harkar kiwon shanu da noma amma ya daina saboda ba su kawo masa kudin shiga ba.

Ya ce ya yanke shawarar shiga satar mutane ne “saboda hanya ce mai sauki ta samun kudi.” “Maganar gaskiya ita ce ba ma samun kudi da yawa daga kiwon shanu kuma mutum na bukatar ya zama da saniya tsawon watanni kafin ta isa amfani.

Satar mutane na bayar da kudi cikin sauri,” in ji shi. Da yake bayanin yadda aka yi satar asibitin, ya ce Danshoho, wanda ma’aikatan jinyan suka yi wa farin sani, ya yi kamar ya zo ne don maganin ciwon kai.

Ya ce, “Ina waje. ‘Yan kungiyata, Maigari, Bodejo da sauransu (gaba daya) suka shiga asibitin amma ba su ga darektan ba. Kamar ya ji harbin bindiga ne ya tsere kafin su kai gareshi.

Daga nan sai Maigari ya yanke shawarar sace marasa lafiya biyu da kuma wata nas.

“Bayan an biya fansa, sai na samu N200,000 kuma na fusata. Na yi barazanar tona musu asiri idan ba su ba ni karin kaso ba.

Labarai Makamanta