Nasarawa: Rashin Cika Alkawari Ya Sa Deligates Fito Na Fito Da Dan Takarar Sanata

Daga Ishaq Saeed Hamza

Kimanin makwannin biyu ke nan da kammala zaben fidda gwani na ɗan kujerar sanata mai wakiltar Nasarawa ta yamma kujerar da shugaban jamiyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya bari bayan zama shugaban jamiyyar APC na kasa.

‘Yan siyasa uku ne suka yi hankoron samun nasarar gadar Abdullahi Adamu da suka hada da
Honorabul Aliyu Wadada (Sarkin Yaƙin Keffi)
Honorabul Arch Shehu Tukur (Sarkin Fadan Keffi)
Hon Barr. Labaran Magaji (Matawallen Toto).

Kafin akai ga zaben fidda gwanin Honorabul Aliyu Wadada ya sanar da janye takararsa ‘yan awanni gabanin zaben bisa zargin rashin adalci da yace ake shirin yi masa hada da zargin da yayi wa jiga jigan jamiyyar APCn Jihar na canza sunayen masu zabe da kin bashi damar ganawa dasu

Honorabul  Barr. Labaran Magaji (Matawallen Toto) kuwa ƙeƙashe kasa yayi tare da shan alwashin ganin abin da zai ture wa Buzu nadi, ya ƙi janyewa ya kuma kasa ya tsare har ta kai ga sake zaben wanda daga bisani aka gudanar a jami’ar Jihar Nasarawa dake karamar Hukumar Keffi, wanda Honorabul Shehu Tukur yayi nasara.

Wannan zaben fidda gwanin ya bar baya da kura domin kuwa tuni Honorabul Aliyu Wadada ya fice daga jamiyyar APC ta hanyar rubuta takardar ficewa daga jamiyyar wa mazabarsa ta Tudun kofa Dake ƙaramar Hukumar Keffi, wata majiya mai tushe ta ayyana Wadada ya koma jamiyyar SDP mai alamar Doki domin takarar kujerar sanata

Wasu daga cikin Delegates din da wakilinmu ya zanta dasu wadanda suka yi zabe  musamman na karamar Hukumar Keffi wadanda suka nemi a sakaya sunansu, sun nuna rashin jin dadinsu na rashin cika musu alkawarin da ɗan takarar jamiyyar APCn Honorabul Shehu Tukur yayi wanda yace zai basu Babura da wasu kudin da basu fadi adadinsu ba in har suka zabe shi yakai ga Nasara sai dai a cewarsu sun ji shiru tun bayan kammala zabe.

Dukkanin kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin ɗan takarar Sanatan abin ya gagara, har zuwa lokacin rubuta rahoton.

Labarai Makamanta