Nasarawa: Matasa Sun Yi Wa Shugaban APC Ature

Rahotannin dake shigo mana daga Lafiya babban birnin Jihar Nasarawa na bayyana cewar wasu fusatattun Matasa sun yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ihu a yayin wani gangamin taron Jam’iyyar da ya gudana a jihar.

Shugaban IPAC mai kula da harkar jam’iyyu a jihar Nasarawa, Cletus Ogah Doma ya yi tir da abin da Matasan suka aikata inda yace ko kaɗan wannan ba abu ne da za a lamunce sake faruwar hakan anan gaba.

Sai dai ya yi ƙarin haske akan labarin da ake yaɗawa na cewar Matasan sun yi yunkurin yi wa shugaban na APC tsirara, inda yace ba haka bane wani jigon jamiyyar ne mai suna Abubakar Abu Giza aka yi wa tozarcin.

Ogah Doma ya yi gargadin matasan jihar Nasarawa a kan shiga bangar siyasa, yace yin hakan bai dace ba. Doma yace bai kamata a rika amfani da manyan gobe wajen rigimar siyasa ba, yake cewa a duk lokacin da aka samu sabani, bai dace matasa su shiga ba.

Doma wanda shi ne shugaban jam’iyyar Zenith Party ya kira abin da aka yi wa jagoran na APC a matsayin dabbanci, yace dole ne ayi tir da danyen aikin. Shugaban ya bada shawara ga APC mai mulki da sauran jam’iyyun siyasa su fito duk suyi Allah-wadai da abin da ya faru, musamman ganin zabe ya zo.

Labarai Makamanta