Nasarata Nasarar Matasa Ce – Sabon Shugaban Matasan PDP

Zababben shugaban matasa na jam’iyyar PDP na kasa, Muhammed Kadade Suleiman, ya ce nasararsa alama ce mai nuna jam’iyyar na damawa da matasa da sanya su cikin mukaman shugabancin jam’iyyar gabanin 2023.

Kadade Ya yi kira ga matasan Najeriya da su shiga jam’iyyar PDP domin ceto kasar nan da kuma ceto makomarsu daga halaka, wanda APC ta tsunduma ciki.

Sabon Shugaban matasan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, ya ce kofarsa a bude take ga kowa, don ba da shawara, gudummawa da goyon baya.

Ya ce, duk wannan zai yi ne domin gudanar da ayyukansa kamar yadda ya yi alkawarin aiki don tabbatar da burin PDP na komawa kan karagar mulki a shekarar zabe ta 2023.

“A karkashin jagorancin sabon shugabanmu da aka zaba, Dr Iyorchia Ayu, ni da sauran zababbun mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC), za mu yi aiki tukuru don mayar da PDP zuwa Aso Rock a 2023.”

Ya kuma bayar da tabbacin cewa, suna sane da irin kalubalen da matasa ke fuskanta a halin yanzu da rashin tafiyar da gwamnati da APC ke fuskanta, inda ya kara da cewa: “Ko kun zabe ni ko ba ku zabe ni ba, ko kun goyi bayana ko ba ku ba goyi bayana ba, ina so in tabbatar muku cewa wannan nasara ce ba ga ni kadai ba, nasara ce ga daukacin jam’iyyar PDP da kuma matasan Najeriya.”

Labarai Makamanta