Nasara Akan Boko Haram: Shekau Ya Barke Da Kuka!

A cikin wani sabon sako na daukan sauti, an ji muryar jagoran kungiyar ta’adda ta Boko Haram, Abubakar Shekau, yana rusa kuka yana neman kariyar Allah daga sojojin Najeriya.

A baya bayan nan, babu sassauci rundunar sojojin Najeriya ta kara kaimi wajen kai hare-hare, tare da samun jerin nasarori a kan ‘yan Boko Haram musamman a yankunan da ke gabar tafkin Chadi.

Cikin sakon daukan sauti na tsawon minti daya da dakiku 22 da jaridar Daily Nigerian ta saurara, an ji muryar Shekau cikin harshen Kanuri yana neman kariyar Allah daga wutar da sojojin Najeriya suka kunno masa.

Shekau ya misalta matsin lambar da sojojin Najeriya suka yi masa a matsayin ‘aikin shaidan’, lamarin da ya ce shi da mabiyansa suna cikin mawuyacin hali a wannan wata mai Albarka na Ramadana.

“In dai zaluncin sojojin Najeriya ne, to Ya Allah ka tsare mu daga sharrrinsu. Ya Allah ka tabbatar da mu a kan addininka. Ya Allah babu abin da muka sani kuma babu abin da zamu iya isarwa kawunanmu. Kai ne mai jibintar lamarin Ya Ubanginjinmu.”

“Mun kaurace wa Izala saboda mu yi addininka na gaskiya; mun bar Tijjaniya saboda mu daidaita a kan tafarkin ka na gaskiya; mun barranta daga Shi’a domin yin addininka na gaskiya; mun bar iyayenmu da ‘yan uwanmu domin mu tsira da addininka na gaskiya.”

Saboda addininka muke yanka wuyan bayinka da wuka; amma a yau suna kokarin sauya mu zuwa wani addini sabanin naka.

Ya Ubangiji kayi mana rahama domin falalar watan Ramadan; Ya Allah ka kawo mana sauki a cikin wannan wata mai Albarka. “Ya Allah ka bamu nasara a kan makiyanmu.

Ya ku yan’uwa don Allah, ku yiwa Allah biyayya ku taimaka min da addu’o’i ta neman kariyarsa.” “Ya Allah ka mu ikon riko da Alkur’ani. Allah kai ne mafi sani.

Tsira da aminci su tabbata a kan Annabin ka, kuma dukkanin godiya ta tabbata a gare ka,” Shekau ya ci gaba da shessheka.

Related posts