Nan Da Wasu ‘Yan Shekaru Arzikin Man Najeriya Zai Kare – Bankin Duniya

Rahoton dake shigo mana yanzu na bayyana cewar Bankin duniya ya bayyana cewa arzikin man feturin kasashe irinsu Najeriya, Ecuador da Chile na da kasa da shekaru 50 kafin ya kare gaba daya.

Shiyasa bankin ke baiwa wadannan kasashe shawara su fara neman wasu hanyoyin zuba jari da samun kudi irinsu sashen Ilmi, cigaban zamani kafin lokaci ya kure.

Wannan na kunshe cikin rahoton da Bankin duniyan ya saki ranar Laraba, 27 ga Oktoba, 2021, mai taken “Canzawar arzikin kasashe a shekarar 2021.”

A rahoton da Jaridar Leadership ta tattaro, na bayyana cewar muddin ba’a samu wasu sabbin rijiyoyin man fetur ba a Najeriya, to wadanda ake hakar mai zasu bushe nan da shekaru 49 amma dai arzikin Gas zai rage.

Rahoton ya kara bayani kan wasu kasashe 18 da arzikin man feturinsu zai kai shekaru sama da 200 kafin ya kare.

“Kasashe masu arzikin mai irinsu Najeriya da Ecuador ka iya karar da arzikin man feturinsu nan da shekaru 50 dubi ga yadda suka diba yanzu, muddin ba’a samu wasu sabbin rijiyoyin mai ba.”

“Kasashe masu arziki irin wannan basu yi amfani da kudaden da suke samu ta hanyar da ya dace ba.” “Idan aka cigaba da kashe kudaden haka, zai shafi arzikin wadannan kasashe ranar gobe.”

Labarai Makamanta