Najeriya Za Ta Taimaki Sudan Ta Kudu A Yaki Da ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin taimaka wa ƙasar Sudan ta Kudu a yaƙi da ‘yan bindiga da kuma haɗin kan ƙasar.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake karɓar baƙuncin wakilin Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

“Za mu duba halin da kuke ciki don ganin yadda za mu taimaka,” inji Buhari cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar.

Wakilin na musamman ya yi wa Buhari bayani kan yadda wata ƙungiyar masu ta da ƙayar baya “kamar Boko Haram ta aikata kashe-kashe da wulaƙanta jama’a da lalata dukiyoyi.

Sanarwar ta ƙara da cewa daga baya kuma ya nemi “haɗin gwiwa kan tsaro, musamman ba wa dakaru horo tun da kuna da ƙwarewa kan wannan lamari”.

Labarai Makamanta