Najeriya Za Ta Kasance Kan Gaba Wajen Fitar Da Shinkafa Waje – Ministan Noma

Ministan aikin gona da raya karkara, Sabo Nanono, ya ce a yanayin habakar noma da sarrafa shinkafa da ke faruwa a Najeriya, Najeriya zata fara fitar da shinkafa nan da shekaru biyu masu zuwa.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a garin Kura, jihar Kano. Ya kai ziyara ne duba rawar da garkame iyakokin kasar nan ta taka a bangaren noman shinkafa a kasar nan.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Nanono da ministan al’adu da yada labarai, Lai Mohammed, sun jagoranci masu ruwa da tsaki da kuma kungiyar ‘yan jaridu don duba kamfanonin gyaran shinkafa da ke Kura.

Kungiyar ta kai ziyara ga wasu kamfanonin hadin guiwa na sarrafa shinkafa a jihar. Kamfanonin sun hada da Al-Hamsad, Kura Bothers, Tiamin Rice Ltd da Umza Internationa Farms.

“Ta yadda noman shinkafa ke habaka a Najeriya, nan da shekaru biyu masu zuwa zamu fara fitar da shinkafa kasashen ketare don siyarwa,” “Ga wadanda ke fargabar rufe iyakokin kasar nan da aka yi, ba mun yi hakan ne don musgunawa mutane ba.

Mun yi hakan ne don kare makomar kasarmu, samar da aiyukan yi da kuma samar da isasshen abinci, Gwamnati zata cigaba da ba wa manoman shinkafa goyon baya don cimma nasara,” cewar ministan.

Related posts