Gwamnatin Amurka ta sanya hannu kan takardan yarjejeniyar tallafin Dala Biliyan 2.1 ($2.1 billion) ga Najeriya domin taimaka mata wajen farfadowa daga annobar COVID-19 da kuma tattalin arziki.
Wannan ya faru ne lokacin da Sakataren wajen Amurka, Antony Blinken ya kawo ziyarar aiki Najeriya, a karshen makon da ya gabata.
A hira da manema labarai, Blinken yace wannan tallafi zai taimakawa Najeriya wajen cigaba a bangarorin daban-daban. A jawabin da yayi, yace wannan “babban zuba jari ne wajen inganta ilimi, kiwon lafiya, da wasu ayyukan jin dadi da yan Najeriya ke nema domin nasara a nan gida da kuma waje.”
Blinken ya kara da cewa Amurka na hada kai da Najeriya wajen magance matsalar tsaro, wanda ya hada da Boko Haram, ISWAP da yan bindiga. “A ganawata da shugaban kasa, mataimakin Shugaban kasa, da ministan waje, mun tattauna muhimmancin samar da hanya mai kyau wajen magance matsalar tsattsaurin ra’ayi da kuma kare hakkin dan Adam a Najeriya.”
“Lamarin Najeriya na shafanmu kulli yaumin a Amurka, saboda karfinta a waje.” Mun baku rigakafi guda milyan 7.6 Blinken ya cigaba da cewa Najeriya ta samu kwayar rigakafin Korona guda milyan 7.6 daga Amurka. Yace: “Mun sa ran sake turo adadi mai yawa na rigakafin zuwa karshen shekara, kyauta kuma babu ko sisi.”
You must log in to post a comment.