Najeriya Za Ta Fita Daga Matsalar Tsaro Idan An Zabi Jajirtattun Shugabanni – Kyari

An bayyana cewar ko shakka babu Najeriya za ta fita daga cikin ƙalubalen matsalar tsaro da take fama dashi muddin ‘yan Najeriya suka zaɓi jajirtattun shugabanni waɗanda suka dace a shekarar zaɓe ta 2023.

Sanata mai wakiltar mazaɓar Borno ta Arewa Sanata Abubakar Kyari ya bayyana hakan a cikin tattaunawar da aka yi da shi a cikin shirin ‘State Of The Union’ wanda gidan talabijin na Liberty Abuja ke gabatarwa a karshen mako.

Kyari ya ƙara da cewar makomar tsaro na hannun ‘yan Najeriya ta hanyar zaɓen Shugabannin da suka dace, bisa ga haka ‘yan Najeriya suyi dubi ga abubuwan da suka faru a baya da waɗanda ake ciki yanzu domin samar da kyakkyawar makoma ga ƙasar a zaben dake tafe.

Ɗan Majalisar ya bayyana cewar a halin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki yanzu, nauyi da ke kan dukkanin jama’ar ƙasar su bada tasu gudummuwar wajen ganin ɗorewar kasar da haɓakar ta gaba ɗaya.

Dangane da halin da makomar harkar tsaro musanman a yankin Arewa maso gabas ke ciki kuwa, Sanata Abubakar Kyari ya yaba ƙoƙarin da jami’an tsaro musanman sojoji ke yi na ganin tsaro ya dawo a yankin, amma duk da haka ya kamata a sake zage damtse sosai domin ceto yankin da sauran wurare a Jihohin Arewa dake fuskantar matsalar tsaro.

“Za a samu nasara a yaƙin da ake yi da ‘yan ta’adda a yankin ne idan ya zamana ana samun haɗin kai a tsakanin jami’an tsaro da inganta su da kayan aiki wanda zai taimaka musu fuskantar abokanan gaba”.

Dangane da cece-kucen da ake yi na sulhu ko rashin sulhu da ‘yan ta’adda Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewar nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati ta tabbatar ta inganta rayuwar jama’arta waɗanda bala’in ‘yan Bindiga ya tarwatsa ya mayar dasu ‘yan gudun hijira, inda ya bayyana cewar babu adalci ace za’a sake ɗaukar wasu kudaɗe aba ‘yan ta’adda da sunan sulhu bayan wancan ta’asa da suka yi hakan bai dace ba.

Daga karshe Sanatan ya yi kira ga Malaman Addini da su cigaba da yin wa’azuzzuka da kiran jama’a akan muhimmancin zaman lafiya da cigaban ƙasa.

Labarai Makamanta