Najeriya Ta Zama Filin Karkashe Mutane – Kukah

A saƙonsa na bikin Ista na wannan shekara ta 2021 Babban Limamin Cocin Katolika na Sakkwato, Bishop Matthew Kukah, ya yi amfani da damar wajen ƙara sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A sakon nasa na Ista na 2021 mai taken, ‘Kafin daukakarmu ta tashi’, malamin ya ce masu tayar da kayar baya suna cin karensu babu babbaka a karkashin kulawar Buhari, ba tare da tsoro ko fargaba ba.

Bishop Kukah ya ƙara da cewa Buhari ya bayyana kungiyar Boko Haram a matsayin wani yanayi na kananan gobara da ke haifar da babban gobara a yayin rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a 2015.

“Yanzu, a karkashin kulawarsa, gobarar tana cin al’ummar, kuma a lokuta da yawa, hakika suna farawa da kaɗan- kaɗan kafin su girma su mamaye ko ina.

“Gaba daya, matsalolin Najeriya na ci gaba da girma a kulla-yaumin, amma dole ne hannayenmu su ci gaba da mikewa cikin addu’a.” ’Yan Najeriya na cikin wani hali mawuyacin hali a karkarshin wannan mulkin.

Bishop din na Katolika ya ce abin da Najeriya ke ciki a halin yanzu shi ne tunatar da halin da Isra’ila ke ciki wanda ya kai ga mutuwar Eli, wanda ya kasance babban malami.

Ya lissafa wasu daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu, wadanda suka hada da rikicin Boko Haram, fashi da makami, satar mutane da sauran muggan laifuka. A cewarsa, wadannan suna haifar da tsoro kan ko “daukakar Najeriya na gab da gushewa”.

Labarai Makamanta