Najeriya Ta Yi Babban Rashi Na Rasuwar Sama’ila Isa Funtuwa – Buhari

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un! A ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, 2020 Allah ya yi wa Alhaji Isma’ila Isa Funtua rasuwa bayan ya samu bugun zuciya.

Isma’ila Isa Funtua ya na cikin manyan na-hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma surukinsa ne bayan abokantakar da ke tsakaninsu.

Shugaban kasar ya yi jawabi ya na nuna takaicin wannan rashi, inda ya aika sakon ta’aziyya ga ‘yanuwan marigayin da kuma mutanen Katsina.

“Cikin takaici, shugaba Muhammadu Buhari ya samu labarin mutuwar tsohon abokinsa kuma na kusa da shi, Malam Isma’ila Isa Funtua, wanda ya kasance shugaba ne na kungiyar NPAN.” Jawabin ya kara da cewa: “Shugaban kasar ya na yi wa iyalai da dangi, da gwamnati da kuma mutanen jihar Katsina da abokai da na-kusa da tsohon shugaban na NPAN, musamman abokansa a harkar aikin jarida ta’aziyyar wannan rashi.”

Buhari ya bayyana marigayin da “Mutumin da ake kauna kuma ake ganin darajarsa.” “Shugaba Buhari ya yi imani cewa mutuwar ‘dan jaridar kuma ‘dan kasuwar ya kirkiri wani wawakeken gibi domn Malam Funtua ya kasance a kullum tare da shi a tafiyarsa ta siyasa.”

Tsohon ministan kasar ya kasance cikin wadanda su ka rika dafawa Muhammadu Buhari har ya kai ga zama shugaban kasar Najeriya bayan shekaru fiye da goma ya na harin kujerar.

“Shugaban kasar ya roki Allah ya karbi baƙuncin Malam Funtua, sannan ya ba iyalinsa juriya da ikon jure wannan rashi.”

Labarai Makamanta