Najeriya Ta Kama Hanyar Rugujewa – Gwamna Ortom

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Binuwai na bayyana cewar Gwamna Samuel Ortom, na jihar ya ce ya dace shugaban kasa ya gane cewa kasar nan na rushewa sakamakon al’amuran ‘yan ta’adda, wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a ƙasar.

A sakon da ya aike wa shugaban kasa Buhari a ranar Asabar domin taya shi murnar cika shekaru 79 a duniya, Nathaniel Ikyur, sakataren yada labarai na Ortom, ya sanar da cewa gwamnan ya ce rashin tsaron da ya addabi mutane ba shi ba ne alkawarin shugaban kasar yayin da ya hau mulki.

Ina kaunar ka amma lokacin daukar mataki ya yi, Najeriya na rugujewa, gwamnan wanda ya ce ya na kaunar Buhari, ya yi kira ga shugaban kasa da ya dauka matakin gaggawa domin tsare kasar nan kafin ya bar kujerarsa.

Labarai Makamanta