Najeriya Ta Fi Karfinka A Yanzu – Babangida Ga Peter Obi

Tsohon gwamnan jihar Neja Alhaji Babangida Aliyu ya bayyanawa ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi cewa ba zai iya mulkar Nijeriya a shekarar 2023 ba.

Inda yace yayi gaggawa kamata yayi ya bari sai a shekarar 2027 ko kuma shekarar 2031 sai ya nemi takarar shugaban kasar.

Babangida ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai na Channels a Abuja, sai dai ya bayyana Peter Obi a matsayin Mutumin kirki.

A karshe Babangida yace da ace Peter Obi bai sauya sheka ba da shi Atiku zai zaba a matsayin abokin takararsa a jam’iyyar PDP.

Labarai Makamanta