Najeriya Na Iya Wargajewa Kafin 2023 – Limamin Katolika

Rahotanni dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na cewar tsohon Shugaban Cocin Katolikan Abuja, John Cardinal Onaiyekan, ya bayyana cewa da yiwuwan Najeriya ta balle kafin 2023 saboda halin da kasar ke ciki.

Ya bayyana cewa Shugabannin Najeriya na son mannewa kan kujeran mulki ko da wa’adinsu ya kare saboda son kai, mugunta da rashin tunani. A hirar da yayi da jaridar Saturday Punch, Limamin ya bayyana cewa daya daga cikin abubuwan dake barazana ga Demokradiyya a Najeriya shine Gwamnatocin dake ci basu son zaben gaskiya da lumana.

“Babu wani dalilin da zai sa a cigaba da fuskantar matsalar tsaro har 2023. Idan ko ba’a shawo kan matsalar ba, hakan na nufin mun ji kunya a matsayin al’umma kuma babu bukatar wani zabe kasar ta watse.”

“Game da zaben kuwa, bamu da tabbacin Najeriya ba zata balle ba. Wadannan matsaloli (na tsaro) ya kamata mu fuskanta yanzu.”

Labarai Makamanta