Najeriya Na Bukatar Megawat Dubu 100 Na Magance Matsalar Lantarki – Minista

Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Farfesa Barth Nnaji, ya bayyana cewa Nijeriya na buƙatar megawat dubu 100 na wuta in har ta na buƙatar magance matsalar wutar lantarki a ƙasar.

Nnaji ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a kan makomar wutar lantarki a ƙasa ranar Juma’a a Enugu.

Ya ce ƙasar na fama da matsaloli wajen samar wa, yaɗa wa da rarraba wutar lantarki a ƙasa.

Ya ce duk wannan shi ne ya sanya zai yi wuya a samu isashshiyar wutar lantarki ga ƴan kasa.

Labarai Makamanta