Najeriya Na Bukatar Agajin Gaggawa Domin Fita Daga Tarnakin Bashi – Bankin Afrika

Shugaban bankin raya kasashen Afrika Akinwumi Adesina ya bayyana cewa Najeriya na bukatar taimako don warware basukan da suka dabaibayeta la’akari da yadda matsalar ke barazana ga ci gaban kasar ta yammacin Afrika.

A jawabinsa yayin taron tattalin arziki da zuba jari a birnin New York Akinwumi Adesina wanda asalinsa dan Najeriya ne da ke jagorancin bankin, ya ce tarin bashi ya yiwa kasar katutu wanda ya zama babban kalubale gareta wajen gudanar da ayyukan ci gaba.

A cewar Adesina ba kadai Najeriya, kasashen Afrika da daman a fama da matsalar basukan da suka yi musu katutu bayan hauhawar yawan bashin da suke karba zuwa kashi 70, wanda ke nuna bukatar da ake da ita ta ganin kassahen Duniya ko dai sun sassauta musu ko kuma sun yafe musu bashin gabaki daya.

Shugaban na bankin raya Afrika, ya ce zuwa yanzu jumullar bashin da ake bin Najeriya ya haura Naira tiriliyan 42 ko kuma dala biliyan 103 da adadin dala biliyan 40 da ta ciwo daga waje, wanda a cewarsa, tabbas kasar na bukatar taimako don warware wannan matsala da ta dabaibayeta.

A cewar Akinwumi Adesina, Afrika na bukatar taimako da kuma hada hannu da manyan kasashe wajen magance dumamar yanayin da ke yiwa nahiyar barazana, yayinda ya koka da matsalar rashin zuba jari a Najeriya.

Adesina ya bayyana cewa yanzu haka kasar na bukatar zuba jarin dala biliyan 759 nan da shekarar 2043.

Labarai Makamanta