Najeriya Na Bukatar Addu’a – Honorabul Kero

Wani jigo Kuma daya daga cikin masu ruwa tsaki a babban Jam’iyyar adawa ta PDP reshen kaduma kuma ‘dan takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltan Mazabar Kaduna ta kudu a zaben 2023, Hon Hussaini Wanda akafi sani da KERO ya bakaci daukacin al’umar musulmi da kirista da suyi anfani da lokacin bukukuwan sabuwar shekara da sauran ibadun su wurin yin addu’a ba dare ba rana musamman dan samun saukin shakakin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da ya haifar da hauhawan kayayyakin masarufi ga mafi yawancin ‘yan Najeriya.

Hon KERO ya bayyana hakan ne yayin karban karramawar da gidauniyar SM Gamji foundation Mai Taimakawa marayu da masu karamin karfi ta bashi a Kaduna wanda Hajiya Suhaima ke shugaban ta.

A nata jawabin Hajiya Suhaima M Gamji “tace akwai ‘yan siyasa kala kala a Kaduna Amman sun zabi su karrama hon Hussaini Abdulkareem Kero ne saboda kokarin sa na ganin ya inganta rayuwar matasan karamar hukumar Kaduna ta kudu da Jihar Baki daya da yakeyi Babu dare babu Rana Kuma ba tare da duba inda ka fito a siyasance ba kamin ya Taimakeka. Kuma wannan hali na Taimakon al’uma ba tareda nunawa kowa banbancin addini ko kabilanci ba shiyasa muka karrama shi.domin kara masa kwarin gwuiwa da Kuma kalulbalantar sauran Yan Siyasa dasu dinga koyi da kyawawan halin KERO:”Inji Hajiya Suhaima

Shima a nashi bangaren Hon KERO ya nuna jin dadin sa Kuma yayiwa ƙungiya SM Gamji alkawarin kasancewa daya daga cikin iyayen gidauniyar wacce aka ginata domin ganin an tallafawa marayu da sauran marasa galinu domin Suma su samu Ilimin da zasu anfani kansu da Kuma Yankin mu na arewa. Kuma yayi wa gidauniyar alkawarin bada gudunmuwar sa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso

Daga karshe Hon Hussaini Abdulkareem Kero ya shawarci dukkan ‘ yan dasu kauda duk wani banbancin akida mu taru mu yiwa kasar mu Najeriya domin aikin zaman lafiya aikine da ya shafemu ba gwamnatin tarayya kadai ba.

Ina Addua a madadina da dukkan masoyana wanda na sani da wanda ban sani da Allah ya kawowa kasarmu Najeriya dawwamanmen zaman lafiya da karuwar wadadatar tattalin arziki da zai ragewa ‘yan Najeriya radadin kuncin da suke ciki. Kuma Allah SWA nake roko yasa wannan shekara Tafi Wanda ta Gabata na 2021.

Labarai Makamanta