Najeriya Da Turkiyya Za Su Hada Karfi A Yakar Matsalar Tsaro – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya na bayyana cewar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ke ziyarar aiki a kasar ya ce ƙasar ta yi alƙawalin taimakawa Najeriya magance ƙalubalen tsaro da ke damunta.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce shugaban Turkiyya ne ya yi tayin taimakawa Najeriya kan fannin sha’anin tsaro.

“A ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya za ta haɗa gwiwa da Turkiyya wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta,” in ji sanarwar.

A cewar sanarwar shugaba Buhari ya yi godiya ga shugaban Turkiyya kuma a ganawar da shugabannin biyu suka yi ya shaida masa cewa, Turkiyya ta samu ƙwarewa sosai wajen tunkarar ƙalubalen tsaro iri daban-daban kuma Najeriya za ta amfana da ƙwarewa.

Labarai Makamanta