Najeriya Da Faransa Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Inganta Kasuwancin Noma

Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu akan wata yarjejeniya da ofishin Jakadancin Faransa da Hukumar Ci gaban Faransa ta AFD da kuma kamfanin Semmaris wadda ta kunshi kudin da ya kai euro miliyan guda da dubu 200 domin gudanar da bincike akan yadda za’a inganta kasuwancin amfani gona a kasuwannin Najeriya.

Wannan kudi da Hukumar AFD zata zuba zai bada damar gudanar da bincike na shekara guda akan yadda za’a taimakawa ma’aikatar noma da raya karkarar Najeriya akan yadda zata samar da wasu kasuwannin na musamman domin sayar da amfanin gonakin da ake nomawa a kasar.

Binciken na shekara guda wanda zai fara daga watanni 3 na farkon wannan shekara zuwa watanni 3 na farkon shekara mai zuwa, zai mayar da hankali ne akan yadda ake cinikin amfanin gona daga yankunan karkara zuwa birane, yayin da zai mayar da hankali akan manyan yankuna 3 da akafi cinikin amfanin gonakin da suka hada da Lagos zuwa Ibadan da kuma Kano zuwa Kaduna, sai kuma Owerri zuwa Fatakwal.

Binciken zai bada damar nazari akan kasuwannin da ake da su yanzu da zurfafa bincike akan yadda ake safarar amfanin gonakin zuwa kasuwanni da dokokin da ake amfani da su a kasuwannin, domin bada shawarwarin yadda za’a inganta su wajen gina sabbin manyan kasuwanni guda 3.

Yarjejeniyar ta ce bayan kammala nazarin, kamfanin Semmaris na Faransa zai aiwatar da shawarwarin da aka bashi tare da taimakon wasu hukumomin ma’aikatar kula da ayyukan noma da raya karkara na Najeriya.

Kamfanin Semmaris ya kwashe sama da shekaru 50 yana gudanar da irin wadannan kasuwannin amfanin gona a duniya baki daya daga Rugis dake kasar Faransa, yayin da yake aiki tare da wasu kamfanoni sama da 1,200.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Shidai wannan sabon tsari zai dora ne akan shirin tallafin Bankin duniya da AFD na shekaru 10 wanda suka zuba jarin da ya kai euro miliyan 700, ciki harda miliyan 296 da AFD ya bayar.

Bangaren noma na samar da kashi 22 na tattalin arzikin Najeriya, yayin da yake dauke da kashi 70 na kwararrun ma’aikata da wadanda ba kwararru ba.

Najeriya na sahun gaba a duniya wajen noman rogo da doya da masara da shinkafa da gero da koko da kuma manja.

Wadanda suka jagoranci bikin sanya hannu akan yarjejeniyar sun hada da ministan noman Najeriya Mohammed Mahmood Abubakar da ministan kudi Zainab Shamsuna Ahmed da Jakadiyar Faransa a Najeriya Emmanuelle Blatmann da kuma wakilin AFD.

Labarai Makamanta