Najeriya Ce Sahun Gaba Wajen Yawan Matalauta A Duniya – El Rufa’i

An bayyana cewar Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace kasa fama da talauci da kuma yawan matalauta a faɗin duniya gaba daya, kuma lamarin ya ƙara ta’azzara a cikin ‘yan shekarun nan.

Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi wannan bayanin ne a lokacin kaddamar da Hukumar Kula da Kare Lafiyar Jama’a a jihar ranar Talata.

El Rufa’i ya ce gwamnatinsa ta kafa hukumar ne don tabbatar da cewa duk shirye-shiryen kula da kare rayuwa da zamantakewa an isar da su cikin hadaka, mai kunshe da ci gaba.

Gwamnan ya ce dole ne a yi amfani da rajistar zamantakewar jama’a don shirye-shiryen da aka tsara don taimaka wa talakawa. Ya kuma roki kasar da ta yi watsi da batun bayar da guraben shirye-shiryen tallafawa talakawa a hannun masu kudi.

“Najeriya na cikin lokutan jarrabawa. Muna da mafi yawan matalauta fiye da kowace ƙasa a duniya. “Duk da haka, duk lokacin da aka tsara wani shiri don taimakawa talakawa da marasa karfi, sai a samu akasi inda ake ware muhimman mutane maimakon duba ga wadancan matalautan da marasa karfi wadanda suka cancanta.

“Wannan abin takaici ne. Dole ne mu kaurace wa tunanin gurbi kuma mu yi amfani da rajistarmu ta sada zumunta don bayar da tallafi ga wadanda suke bukatar hakan da gaske,” inji shi.

Ya yi kira ga fitattun ‘yan siyasa da cewa “don Allah a sauke wannan tunanin” kuma a yi amfani da rajistar zamantakewar jama’a, don haka, shirye-shiryen da ake duba ga masu rauni su isa gare su.

Labarai Makamanta