Najeriya Ce Kasar Da Tafi Cancantar A Zuba Hannun Jari A Cikinta – Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ce ta fi dacewa da ƙasar da masu zuba hannun jari daga Amurka za su zuba kudadensu.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Washington DC yayin da yake wata tattaunawa ta musamman ta kasuwanci tsakanin Amurka da Najeriya da kuma zauren masu zuba hannun jari, a wani taro da kungiyar hadinkan Amurka da Afrika ta shirya tare da hadin gwiwar ma’aikatar kasuwanci da zuba jari, a gefen taron shugabannin Afrika da Amurka.

Yace baya ga yawan da kasar ke da shi bugu da kari tana da fadin kasa wanda shi ma wani abun tutiya ne, ya kuma zayyano wasu damarmaki da Najeriyan ke da su, wanda ya sa ta zama wurin da ya fi dacewa azuba hannun jari.

Cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaban ya fitar, ya ce “yana da matukar kyau in maimaita wannan, cewa Najeriya na da faffadan tattalin arziki.

Kuma na farko tana da yawan al’umma ita ce tafi kowacce kasar Afrika karfin tattalin arziki, babu shakka kuma Najeriya ce kan gaba wajen sayen kayayyaki da ake kai wa nahiyar.”

Labarai Makamanta