Najeriya Ba Za Ta Wargaje Ba – Babangida

Tsohon Shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) ya shawarci al’ummar kasar su zama masu kwarin gwiwa da kyakkyawan fata duk da matsalolin da ƙasar ke ciki.

Najeriya, in ji shi, za ta ci gaba da kasancewa dunkulalliyar kasa guda.

Janar Babangida na wannan jawabi lokacin zantawa da manema labarai a Minna kafin bikin cikar Najeriya shekara 62 da samun ‘yanci, kamar yadda Gidan Talbijin na Channels ya ruwaito.

Don ganin haka, Janar Babangida ya ce akwai bukatar kowa ya kara himma.

Ya yaba wa kokarin gwamnatoci daban-daban a Najeriya wajen ganin kasar ta ci gaba da zama dunkulalliya, ya kuma yi kira don samun karin nasarori.

Ya ce burinsa shi ne ya ga Najeriya ta zama kasa mai karfi da yalwar arziki da hadin kai ta yadda zaman lafiya zai zarce komai.

Labarai Makamanta