Najeriya Ba Za Ta Juri Zaluncin APC Ba – Tambuwal

Gwamnonin jam’iyyar PDP sun ce Najeriya ba za ta iya jure wasu shekaru hudu a karkashin jam’iyyar APC ba.

Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana hakan a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba a wajen bude wani taron jam’iyyar na kwana biyu.

Taken taron shine “Lokaci yayi da za a ceto da kuma sake gina Najeriya.”

Tambuwal ya kara da cewar ya zama dole Najeriya ta rungumi garambawul domin tsira, daga halin barazanar da kasar ke fuskanta.

Labarai Makamanta