Najeriya Ba Za Ta Durkushe Saboda Matsalar Tsaro Ba – Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce yana da yakinin cewa matsalolin tsaron da ake fama da su a sassan kasar ba za su ga bayan Najeriya ba har ta kai ta durkushe yana mai cewa kasar za ta fita daga kangin da ta tsinci kanta a ciki.

Ya bayyana haka ne a wani taro da aka yi domin karrama shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN wato Dakta Samson Ayokunle.

A jawabinsa, Obasanjo ya ce yana da imanin cewa Najeriya ba za ta durkushe ba duk da karuwar tabarbarewar tsaro.

Ba Obasanjo ne kadai yake da irin wannan fahimta ba, wasu gwamnoni da suka halarci taron irinsu Dapo Abiodun na Ogun da Seyi Makinde na Oyo na ganin za a samu mafita.

Labarai Makamanta