Najeriya Ba Ta Taba Yin Gwamnati Mara Kan Gado Kamar Ta Buhari Ba – Soyinka

Fitaccen marubucin Duniya, Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya ba ta taɓa shaida gwamnati mara alkibla kamar gwamnati dake ci yanzu ta Buhari ba, kasar ta kama hanyar rugurgujewa, sannan gwamnati mai-ci ba ta da lakanin gyara.

Farfesa Soyinka ya yi wannan magana a Freedom Park, jihar Legas yayin da yake tattaunawa kan taɓarɓarewar tsaro da koma bayan takunkumin da aka kakabawa matafiya saboda cutar COVID-19.

An yi wa taron da aka yi a Legas take da: “COVID-19, fasaha da fatattakar mutanen gari.” “Matsalar ita ce gwamnatin nan ba ta fahimci matsalolin da ke Najeriya ba. Idan muna jiran gwanatin nan ta kawo mafita, to muna cikin rudu.”

“Muna cikin wani irin mummunan yanayi. Kasar nan na cikin wani hali. Tana sukurkucewa a gaban idanmu, kuma Gwamnatin nan ta rude.”

Soyinka ya fadawa gwamnatin Najeriya cewa kuci-kucin dabarun da ta dauko na shawo kan matsalolin kasar nan ba za su taba yin aiki a halin da ake ciki ba.

A cewar Soyinka, yadda za a shawo kan matsalolin da suka yi katutu shi ne a kira taron kasa, ta yadda kowace kabila za ta samu wakili da zai bada shawararsa.

Marubucin ya bada labarin wahalar da ya sha a hannun jami’an Najeriya a lokacin da zai yi tafiya zuwa kasar Faransa, yace lamarinsu babu tsari. Ana fama da COVID-19, Dattijon mai shekaru 87 ya yi wata tafiya zuwa Faris da bai ji dadinta ba.

Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya tana neman ta wargaje, ana ji-ana gani, an gagara yin komai, mun tsaya kallon ruwa har kwaɗo zai yi mana ƙafa.

Labarai Makamanta