Najeriya Ba Ta Cancanci Tsoratarwa Daga Ƙasashen Yamma Ba – Ministan Tsaro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ninistan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya ce addu’a Najeriya ke bukata daga gwamnatin Amurka maimakon gargaɗi wanda ya jefa mutane cikin rudani.

Ministan ya bayyana cewa gargadin da Amurka tayi kan yuwuwar kai harin ta’addanci a Abuja ya jefa jama’a cikin tsoro sannan ya razanar da yan Najeriya ta yadda har sun gaza daukar matakin da ya dace.

Sai dai kuma, ya bayyana cewa barazanar bai yi tsanani ba, yana mai bayar da tabbacin cewa gwamnati na kan lamarin da taimakon hukumomin tsaro da na leken asiri.

Magashi ya yi magana ne yayin da yake kare kasafin kudin ma’aikatar tsaro na 2023 a gaban kwamitin majalisar wakilai ranar talata a Abuja.

Jawabinsa martani ne kai tsaye ga wata tambaya da shugaban kwamitin majalisar, Hon. Babajimi Banson yayi kan abun da yake yi don magance gargadin da wasu kasashen waje ciki harda Amurka suka yi kan tsaro.

Magashi ya ce: “Idan kun tuna, a jiya kwamitin tsaro sun gana sannan mun tattauna wannan barazanar kuma mun yarda cewa ba abu ne da zamu yiwa rikon sakainar kashi ba. Mun yi kokarin tabbatar da tushen barazanar ko jawabin da gwamnatin Amurka tayi.

Mun yi kokarin gano kasashen da ke da ra’ayi a jawabin da gwamnatin Amurka tayi kuma mun ga cewa hanya mafi dacewa da za a bi da lamarin shine ci gaba da tsaurara matakan tsaro a Abuja da jihohin da ke makwabtaka, wato Nasarawa, Neja da sauransu.

“Sai dai kuma, mun yarda cewa ruwa baya tsami banza kuma dangane da hakan, mun yi nasarar gabatar da lamarin ga hukumomin leken asirinmu kuma sun gabatar da amsoshi a wuraren da gwamnati ke shakku kuma mun gano cewa muna bukatar sanya idanu sosai don hana duk wasu ayyukan yan bindiga, wanda daga nan ne barazanar zai iya faruwa, za mu samar da isassun runduna da za su iya kawar da irin wadannan lamuran. “Ina mai ba mambobin majalisa tabbacin cewa gwamnati na kan lamarin.

Labarai Makamanta