Naira 234 Ya Kamata A Sayar Da Litar Mai Ba 162 Ba – NNPC

Shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPC, Mele Kyari ya ce gwamnatin tarayya na biyan naira biliyan 120 a kowanne wata a matsayin tallafin man fetur.

Kyari ya fadi hakan ne a taro na musamman da ministoci ke yi wa maneman labarai bayani karo na biyar da aka gudanar a fadar gwamnatin Najeriya a Abuja.

An ruwaito cewa Kyari ya ce, a maimakon ‘ƴan ƙasar su dinga sayen mai kan yadda farashin kuɗaɗen shigo da adana shi suke na naira 234 kan kowace lita guda, gwamnati na sayar da man a kan naira 162, don haka ita ke ɗaukan nauyin cikon kuɗin.

Sai dai ya ƙara da cewa, NNPC ba zai iya ci gaba da asarar waɗanan kuɗaɗe ba, don hakan ‘ƴan Najeriya nan bada jimawa ba za su koma sayen man yada aka samo shi.

Ya kuma shaida cewa dole ne a bar kasuwa ta ƙayyade yada farashin mai zai kasance a ƙasar.

Labarai Makamanta