Nafisa Ta Shiga Jerin Manyan Jaruman Fina-Finai A Najeriya

Tauraruwar fina-finan Hausa Kannywood Nafisa Abdullahi na daya daga cikin jaruman da ake yawan nema a Google 2021 a Najeriya.

Dimokuradiyya ta rawaito cewa Tauraruwar Labarina ta shiga sahun jaruman Nollywood na Najeriya kamar su Destiny Etiko, Tonto Dikeh da Zubby Michael.

Ita ce ta shida a rukunin taurarin fim bayan Destiny Etiko, Zubby Michael, Pere, Tonto Dikeh, Iyabo Ojo da Olu Jacobs.

Haka kuma, Nafisa ita ce tauraruwar Kannywood daya tilo da ta samu matsayi na 10 a fagen bincike na Google.

Duk da cewa Google ya ware Nafisa a bangaren Nollywood maimakon Kannywood, kamar yadda a lokacin da aka buga wannan rahoto.

Sai kuma Rahama Sadau, Fati Washa, Maryam Yahaya da Hadiza Gabon.

Har ila yau, shafin yana da sunan rukuni, tare da ƙungiyar mawaƙa da waƙa da kanta da wasanni da ƴan wasan kwaikwayo da kuma fina-finai da kansu tare da tambayoyin da aka fi yawan yi.

Nafisa tana da mabiya miliyan biyu a Instagram da 176,600 a Twitter da kuma wasu miliyan biyu a shafin Facebook.

Labarai Makamanta