Nadin Ahmad Bamalli: Tsohon Wazirin Zazzau Ya Maka El-Rufa’i Kotu

Tsohon Wazirin masarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu, ya maka Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, masarautar Zazzau da kuma wasu mutane 12 a gaban babbar kotun jihar.

Aminu, ya maka su ne a gaban kotun a kan nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19.

Aminu, wanda na daya daga cikin masu nada sarki a masarautar Zazzau, ya bukaci kotun ta soke martaba Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau.

Da aka gabatar da karar a ranar Laraba wasu daga cikin wadanda Aminu ya maka a gaban kotun akwai sarkin da marigayi Limamin Kona, Malam Sani Aliyu, wand a ya rasu a watan Yulin 2022.

El-Rufai ne dai ya nada Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau a ranar 7 ga watan Okutobar 2020, wanda a baya ya kasance jakadan Nijeriya ne a kasar Thailand.

A lokacin da aka gabatar da karar alkalin kotun mai shari’a Isah Aliyu, ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Fabirairun 2023 don a bai wa lauyan wanda ake kakar damar yin nazari a kan karar tare da kuma gabatar wa da kotun hujjarsa a kan karar.

A tattaunawarsa da manema labarai jim kadan bayan zaman kotun, lauyan da ke tsayawa mai karar Barista Rabiu Saidu, ya ce, wanda yake tsayawa ya shigar da kakar ne saboda sauran wadanda suka kasance masu nada sarki, ba a ba su damar zabo wanda zai zama sarkin ba, inda hakan ya sabawa ala’adar nasarautar.

Ya kara da cewa, a bisa ka’ida masu zabo wanda zai zama sarkin, na tura wa gwamna sunayen wadanda za a nada a matsayin sarkin masarautar, inda ya ce, wanda a yanzu yake a kan karagar masarautar, sunansa baya a cikin sunayen da aka turawa gwamnan, saboda haka bai dace a nada shi sarkin ba, domin nadinsa, ya saba wa shawarar da masu zabo sarkin suka bayar.

Lauya mai tsaya wa masarautar Zazzau, Barista Aminu Usman Bamalli, ya ce, lauyan mai karar ya kamata ya gabatar da adireshin da zai kasance shi mazaunin ne a Kaduna kamar yadda doka ta 4 da ta 6 a tsarin aikin kotun jihar ta tanadar, inda ya ce, amma lauyan, ya kasance mazaunin Abuja ne kuma hakan zai yi matukar wahala a gare su wajen gabatar masa da takardunsu a kan lokaci.

Kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 23 ga watan Fabirairun 2023.

Labarai Makamanta