Na Yi Nadamar Haihuwar Shekau – Mahaifiyar Marigayi Shugaban Boko Haram

Labarin dake shigo mana daga Jihar Borno na bayyana cewar Malama Fatima Abubakar, mahaifiyar tsohon shugaban kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, Abubakar Shekau, ta ce bata da masaniya ko ɗanta yana da ‘ya’ya saboda mawuyacin halin da ya jefa kanshi da tsawon lokaci na rashin haduwar su.

Fatima, wacce ta bayana hakan a wata hira da ta yi da Gidan Talabijin na Trust ta ce ko yana raye ko mace, babu wani abu da ke tsakaninta da shi, domin tabbas ta yi nadamar haihuwar shi.

Tsohuwa Fatima ta bayyana cewa Shekau ya jefa ta cikin ukuba har ta kai cewa ta cire rai da shi. Ta ce: “A bangare na, ni na tsuguna na haifi shi, wannan shine abin da kadai ke tsakanin mu. Ko yana da rai ko ya mutu; mun raba jiha.

“Ban taba sanin ko yana da ‘ya’ya ba ko kuma ba shi da su. Ya jefa ni cikin bakin ciki. Allah zai yi hisabi tsakanin mu a ranar gobe kiyama.”

A watan Mayun shekarar 2021, aka kashe Shekau yayin fada tsakaninsa da mayakan kungiyar (ISWAP). Rahotanni sun ce ya halaka kansa a yayin da ya lura mayakan na ISWAP na daf da cin masa da ransa.

Labarai Makamanta