Na Yi Nadamar Goyon Bayan Buhari – Dino Melaye

Sanata Dino Melaye tsohon ɗan Majalisar Dattawan Najeriya da ya wakilci jihar Kogi ta yamma, yace babbar nadamar da ya yi a rayuwarsa ita ce goyon bayan Buhari da ya yi a zaɓen shekarar 2015, kuma ita ce damfarar da ta taba faruwa a Afrika yadda aka goyawa Buhari baya ya samu shugabancin kasa a 2015.

Melaye ya sanar da hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Channels.

SanataMelaye, wanda yanzu dan babbar jam’iyyar adawa ce ta PDP, ya bar jam’iyyar APC a shekarar 2018.

A yayin jawabi a shirin, ya nemi gafarar ‘yan Najeriya bisa ga abin da ya kira goyon bayan Buhari a 2015 inda yace ya taba makancewa, amma yanzu yana gani.

“Bari in fara da mika ban hakuri na ga Ubangiji, wanda ke mulkin duniya da kuma ‘yan Najeriya a kan goyon bayan Buhari da nayi,”.

“Tsarin Buhari na daga cikin babbar damfarar da ta taba faruwa a Afrika. Takarar Buhari ta 2015 ita ce gagarumar damfarar da aka taba kuma daga Afrika ta fito.”

Jigon jam’iyyar PDP yace yana mamakin yadda har yanzu akwai masu goyon bayan shugaban kasan duk da al’amuran da ke faruwa a kasar nan.

Labarai Makamanta