Na Yi Dukkanin Mai Yiwuwa Wajen Gyara Najeriya – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce baya “tsammanin samun wani yabo” daga ‘yan Najeriya bayan kare wa’adin mulkina domin nayi dukkanin mai yiwuwa wajen gyaran ƙasar.

An ruwaito cewa shugaban ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na ƙasa NTA a ranar Alhamis.

Buhari ya ce cikin shekarun da ya yi a kan mulki ya yi abubuwa da dama a Najeriya, kuma ya yi duk abin da zai iya ga Najeriya inda ya kara da cewa “me kuma zan iya kara yi wa wannan kasar?

Ya kuma ce yana fatan lokacin da wa’adinsa zai kare a 2023, ‘yan kasar za su gano cewa ya yi wa kasar kokarin iyawarsa.

“Na yi gwamna, na yi minista yanzu kuma ina shugaban kasa a karo na biyu. Don haka na taka duka wani matsayi na gwamnati, me kuma zan yi wa wannan kasar?” in Buhari.

“Na yi iya kokari na, ina kuma fatan bayan na bar shugabanci, ‘yan Najeriya za su fahimci ne na yi. Bana tsammanin wata godiya amma ina sa ran ‘yan Najeriya za su ce wannan mutumin ya yi mana kokari. wannan nake tsammani daga ‘yan Najeriya.”

Labarai Makamanta