Na Yi Dukkanin Abin Da Zan Iya A Shugabancin Najeriya – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi iya bakin kokarinsa a matsayinsa na shugaban Najeriya.

Shugaban ya shaida hakan ne a Amurka lokacin da yake tarban Sakatare Janar na kungiyar Abu Dhabi, Sheikh Al- Mahfoudh Bin Bayyah da mataimakinsa, Fasto Bob Roberts na Amurka, a wata ziyarar da suka kai masa.

Buhari ya ce Najeriya kasa ce mai yawan al’umma da ke fuskantar kalubale daban-daban, sai dai a tsawon shekarun mulkinsa ya san cewa ya yi iya kokarinsa.

Shugaban ya kuma kara da cewa shawo kan matsalolin matasa su ne kashin-bayan mulkinsa domin samawa kasar makoma mai kyau.

Bin Bayyah ya ce ya ziyarci Buhari ne, domin gayyatarsa taron da gidauniyarsa Abu Dhabi ta shirya domin karrama shugaba saboda rawar da ya taka ta fuskar tsaro da zaman lafiya.

Ya ce ayyukan Buhari kusan sun zo guda da fafutikar gidauniyar na yaki da kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi da tabbatar da zaman lafiya da hadin-kai tsakanin addinai.

Labarai Makamanta