Na Rantse Da Allah Duk Wanda Nace Zai Mutu Gobe Sai Ya Mutu – Shugaban APC

Shugaban riko na jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya bayyana farin cikinsa bisa yadda jam’iyyarsu take kara samun magoya baya daga sassa daban daban na jihar Kano, ya kuma tabbatar da cewa sun kusa yin dukan karshe kan abokan hamayyarsu, da zarar Tambuwal ya kammala tattaka su.

Jaridar Kano Online News , ta rawaito cewa, Abbas ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin tsohon dan takarar gwamnan Kano a zaben da ya gabata na 2019 karkashin jam’iyyar GPN, Abdulkarim A A Zaura, wanda ya koma cikin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano.

‘’Tuntuni mun gama da wadancan mutanen, amma abinda yayi karashe zamu jira Tambuwal ya gama tattaka su, kuma wallahi a wannan harkar ta siyasa, idan nace gobe zaka mutu, to wallahi saika mutu, in nace zaka rayu a wannan siyasar, ince wannan zai rai to zai rai a siyasa.”

A nasa bangaren shima Hon. Abdussalam Abdulkarim AA Zaura, ya bayyana jin dadinsa tare da tabbatar da cewa, zasu bada dukkan gudummawa domin samun nasarar jam’iyyar APC a jihar Kano.

Labarai Makamanta