Na Kusan Haukacewa Bayan Kisan Da IPOB Suka Yi Wa Matata Da ‘Ya’yana -Jibril

Mutumin da IPOB suka kashe wa matarsa mai ciki wata tara da kuma ƴaƴansa huɗu a jihar Anambra ya ce ya ji kamar ya haukace saboda tashin hankalin da ya shiga.

Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne suka kai hari suka kashe mutum 12, ciki har da mace mai ciki wata tara, Harira Jibril da ƴaƴanta huɗu.

Mijin matar kuma mahaifin ƴaƴan dukkanin mata da aka kashe a harin ya shaida wa BBC cewa an kashe matarsa ne da ƴaƴansa a lokacin da suke kan hanyar dawowa daga ziyarar da ta kai, tare da ƴaƴanta a yankin Orumba ta arewa a jihar Anambra.

“Na shiga tashin hankali, saura kaɗan na haukace – kamar an saka ni cikin wuta, haka nake ji saboda zafin da nake ji,” in ji Jibril Ahmed mijin matar.

“Yanzu ina zan fara – yaya zan yi aure har na samu ƴaƴan da Allah ya ba ni waɗanda har sun yi nisa da karatu.”

“Yarana suna da basira amma ga shi yanzu irin ɓarnar da aka yi min, kawai na yi tawakalli ga Allah – Allah zai saka min,” in ji shi.

“An caje ni naira dubu 170 na daukar gawarsu zuwa jihar Adamawa sannan na biya naira dubu 30 a dakin ajiye gawa,” in ji Jibril Ahmed.

Ya ce a cikin satin nan matarsa za ta haihu amma aka kashe ta.

“Iyayen matata sun shiga tashin hankali kuma ina ƙoƙarin tafiya da gawarta domin a binne ta garin iyayenta.”

Ƴan sandan Najeriya sun ce sun kama ƴan bindigar da suka aikata kisan na mutum 12 da suka ƙunshi har da mace mai ciki da ƴaƴanta huɗu.

Labarai Makamanta