Na Kusan Amarcewa Da Fitaccen Jarumin Kannywood – Stella Daɗin Kowa

Beatrice Williams Auta, wadda aka fi sani da Stella a cikin ‘Dadin Kowa’, shiri mai dogon zango na tashar AREWA24 , a tattaunawarta da Aminiya ta bayyana irin gudunmawar da zata bayar a Kannywood, matukar ta samu dama.

An haifi jaruma Stella a jihar Kaduna, amma ‘yar asalin jihar Taraba ce. Jarumar ta ce ta yi karatunta tun daga Firamare zuwa Jami’a a jihar Kaduna, inda ta karanci Harshen Turanci da Wasan Kwaikwayo.

Jarumar ta bayyana addini da kabilanci a matsayin matsalolin da take fuskanta a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood.

Kazalika, ta yi wa masoyanta albishir da cewa nan da wani lokaci zasu samu labarin aurenta da daya daga cikin jaruman Kannywood.

Har wa yau, ta ce idan ta samu dama zata samar da hadin kai a tsakanin jarumai, masu shiryawa, bada umarni da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar.

Sannan ta kara da cewa za ta samar da horo lokaci zuwa lokaci ga wanda suke taimaka wa wajen shirya fim a Kannywood.

Labarai Makamanta