Na Kasa Gane Gidana Saboda Ayyukan El Rufa’i – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Shugaba Buhari ya yaba gami da yin jinjina da ayyukan da gwamnan jihar El Rufa’i ke yi na raya ƙasa.

Shugaba Buhari ya ce da ya zo Kaduna bai gane gidansa ba saboda ayyukan da Gwamna El-Rufai ke ta faman yi na gina ƙasa

Muryoyi ta ruwaito Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace da ya ziyarci Kaduna ya kasa gane ina ne gabas ina ne yamma domin Gwamna Elrufai ya sauya mata fasali da ayyuka.

Shugaban kasar dai yana Kaduna tun a jiya da dare, inda zai yi kwanaki wajen kaddamar da ayyukan raya ƙasa da Gwamna El-Rufai a biranen Kaduna Zariya da Kafanchan.

Labarai Makamanta