Na Jima Ina Karin Kumallo Da Naman Mutane – Aminu Baba Fitaccen Dan Kasuwa A Gusau

Alhaji Aminu Baba, fitaccen dan kasuwan nan da ke sana’ar motoci da sauran ababen hawa a kamfanin Aminchi Motors Gusau, Jihar Zamfara, ya bayyana munanan ayyukan sa.

Baba, wanda ‘yan sanda suka kama, ya amsa laifin ci da sayar da sassan jikin mutane ga wasu da ba a san ko su waye ba. An kama shi ne a makon da ya gabata bisa laifin kashe wani yaro dan shekara 9 a Gusau.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Ayuba N Elkanah, ya ce wanda ake zargin yana da mata uku da ‘ya’ya 19.

Ya ce ya dauki matasa biyu aikin yi domin su rika diban yara maza su kashe masa, kuma sun yi hakan sau biyu, inda suka samu Naira miliyan daya.

“Na biya su Naira 500,000 ga kowane daya daga cikin kashe yaran biyu. Mun cire azzakari, idanu, hanji kuma ni kan ci wadannan gabobin jikin dan Adam na sayar da wasu ga masu bukata,” inji shi.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce dayan wanda ake zargin, Abdulshakur Mohammad, ya amsa cewa wannan shi ne karo na uku da Baba ya ba shi kwangilar samo sassan jikin dan adam.

Ya ce ya samu N500,000, bayan gudanar da aiki na farko da na biyu kafin a kama shi.

Ya ce sun hada kai da Baba da Ahmad Tukur domin su yaudari wanda aka kashe, wanda aka kai shi wani gini da ba a kammala ba.

Mohammad ya ce bayan sun kashe shi ne suka cire masa hanjin sa, gaba, da kuma ido biyu, inda suka kai wa Baba, wanda shi kuma ya ba su Naira 500,000 kamar yadda suka amince.

Makonni biyu da suka gabata ne aka tsinci gawar yaron dan shekara tara mai suna Ahmad Yakubu Aliyu a wani gini da bai kammala ba a unguwar Barakallahu da ke cikin birnin Gusau.

Ahmad ya bace ne jim kadan bayan ya dawo daga makarantar Islamiyya da ke unguwar Gadar Baga a cikin birnin.

Mai ginin ya hango gawar yaron da ya rube a lokacin da ya zo ci gaba da aikin gininsa.

Nan take ya rufe wurin ya kai rahoto ga ‘yan sanda inda daga baya suka tabbatar da kashe Ahmad aka jefar da shi.

Labarai Makamanta