Na Haƙura Da Siyasa – Ɗan Tsohon Shugaban Kasa Murtala

Babban dan gidan tsohon shugaban kasar Najeriya Murtala Muhammed, Abba Risqua Murtala Mohammed ya bayyana aniyarsa a jiya a Kano kan cewa zai bar siyasa ya mayar da hankalinsa kan kasuwancinsa.

Riqua a 2015 ya yi takarar a matsayin mataimakin gwamna a jam’iyyar PDP a Kano tare da Alhaji Sagir Salihu Takai.

Da yake magana da magoya bayansa a Kano, Abba Risqua ya ce babu wanda ya matsa masa lamba ya dauki matakin, a radin kansa ya dauki wannan mataki domin gina rayuwarsa.

A cewarsa “na bar siyasa ne domin na mayar da hankali kan harkokin kasuwanci na.

Lokacin da na yi takara a Kano, na yi ta amfani da kudaden aljihu na ne, lokacin da na koma kan harkokin kasuwanci na sai na tarar ya yi matukar rauni, shi yasa nake son mayar da hankali yanzu kan kasuwanci in huta daga siyasa. Daga baya wani abu ya tabbatar mani da cewa gwara na koma kan kasuwanci.”

Labarai Makamanta