Na Gaji Da Aikata Zina Aure Zan Yi – Jarumar Kudancin Najeriya

Jarumar wasan kwaikwayon Nolywood, Sylvia Ukaatu, ta lashi takobin komawa ga Allah har zuwa lokacin da zata samu mijin aure.

Sylvia Ukaatu ta bayyana hakan ne a hirar da tayi kwanakin nan kuma Allure Vanguard ta ruwaito. Ta yi nadamar biyayya wa Shaidan da tayi shekarun baya kuma yanzu ta shirya tuba da komawa ga Allah.

“Na koma ga Allah. Ba zan sake fifita kudi kan tsoron Allah ba. Dukkan shekarun nan ba tare da biyayya ga Allah ba sun zama aikin banza, shi yasa nayi alkawarin cewa ba zan sake zina ba sai na yi aure.”

“Ina addu’a wannan sabon matsaya da na dauka zai wanke min zunubai na lokacin da nike bin shaidan.”

Jarumar ‘Yar asalin jihar Anambra wacce a baya ta bayyana yadda take son zina sosai a baya kuma ta yi zina da mutane daban-daban. A cewarta:

“Na kasance mai son zina sosai kuma na yi zinace-zinace saboda lokacin rayuwata nike ci….Lokaci ya yi da zan koma ga mahalicci na. Idan lokaci yayi zai bani masoyi na.”

Labarai Makamanta