Na Fuskanci Barazanar Kisa Akan Aikina – Pantami

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami yayi bayanin kalubalen da ya fuskanta saboda ya kawo tsarin NIN wato tsarin haɗa layin waya da shaidar zama ɗan ƙasa.

A ranar Juma’a 16 ga watan Satumba 2022 Jaridar Daily Trust ta yi rahoto Isa Ali Ibrahim Pantami yana cewa ya fuskanci barazanar kisa a kujerar Minista. Pantami yace yunkurin yi wa kowane layin waya rajista da lambar NIN ta jawo masa wannan barazana.

Ministan ya bayyana haka ne a wajen wani taro na musamman da hukumar NIMC mai tattara bayanan ‘yan kasa ta shirya a birnin tarayya Abuja. Barazana har a rediyo A cewar Dr. Isa Pantami, ta kai an fito baro-baro a gidan rediyo ana yi masa barazana, ba don komai ba sai saboda ya shigo da tsarin yin rajistar NIN.

Kamar yadda Ministan ya fada, wannan Barazana bai sa ya janye yunkurinsa ba domin ya san babu mai iko da rayuwar ‘Dan Adam sai Ubangiji.

“Za mu cin ma nasara a bangaren tattalin arzikin zamani ne a lokacin da muka yi kokari wajen ganin mutane sun shiga cikin kundin bayanan kasa. A lokacin da muka fara aikin nan, mutane da-dama sun juya mani baya. An yi wa rayuwata barazana a gidan rediyon BBC saboda shigo da tsarin”.

Labarai Makamanta