Na Dawo Ruwa A Harkar Fim – Jaruma Farida Jalal


An dade ba a ga tsohuwar jaruma Farida Jalal ba cikin harkar fim ba, sai a dan kwanakinnan da a ke ganin ta fara bayyana a cikin wasu wakoki na siyasa, da kuma fina-finan da a ke yin aikin su a wannan lokacin.

Ganin ta fara shiga cikin harkar fim ne wakilin jaridar Dimukaradiyya ya nemi tattaunawa da ita a kan dawowar da ta yi, inda ta ke cewa “Gaskiya haka ne a yanzu na dawo harkar fim duk da dai mutane abin zai ba su mamaki ganin an dade ba a gani na.”inji ta

To ko me ya sa ba a ganin Farida Jalal a cikin harkar fim din tsawon lokaci?

“To a can baya dai na yi aure ne, kuma daga baya da aure na ya mutu sai na koma gefe na fara wakokin yabon Manzon Allah S A W, amma dai a yanzu na dawo ina hadawa duka biyun, da wakokin yabon Manzon Allah S A W da kuma harkar fim.” a cewar ta.

Ko ya ya kika samu harkar da kika dawo bayan tsawon lokaci ba kya cikin ta?

” Eh gaskiya akwai sauyi sosai don wasu da muka yi zamani da su da yawa sun bar harkar, amma dai abin da na gani a yanzu shi ne, harkar fim din ba irin ta da ba ce an samu sauyi sosai, don haka a yanzu Harkar ba irin ta lokacin baya ba ce.” Kamar yadda ya bayyana.

Tun da kin dawo wanne sako za ki bayar ga masoyan ki, don su San cewar Farida Jalal tana tare da su?

” Ina kira ga masoya na cewar a yanzu na dawo harkar fim, kuma Farida Jalal dai da kuma sani a baya ita ce dai ba ta canza ba sai dai Karin shekaru da ta yi, amma dai in sha Allahu ina tare da ku a matsayin jarumar da kuka sani tsawon lokaci, kuma ina yi wa kowa fatan alheri. 

Labarai Makamanta